GABATAR DA MAKARANTAR MISHAN NA CAPRO
Calvary Ministries – Kungiyar bishara ce ta yan kasa, wadda tana aikin bishara a tsakanin
al’ummai ko kabilun da basu da bisharan ko basu koshi ba. CAPRO tana aiki a kabilu da dama a arewacin Nigeria da al’ummai dabandaban a wasu sassanta da kuma a kasashen duniya 36.
Makarantar Mishan Na CAPRO
Makaranta ce inda ake horas da ma’aikatan bishara wadanda
suke da kira zuwa aikin Mishan a al’adu ko kabilu dabandaban.
Mazaunin Makarantar
Tana Kauna (Tsakiya) Gundumar Daddu, Karamar Hukumar Jaba, Jihar Kadunan Nigeria
nature of the training
1. Makarantar share fage -Wata biyar (Domin wadanda basu da cancantar shiga ainihin
Makarantar horaswar).
2. Yaki da jahilci
3. Koyon sana’a ko aikin hannu (2 da 3 Domin matan daliban da basu sami shigan ainihin
horaswan ba).
Tsawon Lokacin Horaswa
Makarantar shekara daya ne (Daga Janairu zuwa Disamba tare da
hutu da zuwa koyon aiki a filin bishara).
Manufan Makarantar
Domin a horas da ma’akatan bishara su sami hali, da ilimi da tarbiya da
basira da ya wajaba ga yin aikin bishara (Mishan) a cikin kabilu ko al’adu daban-daban.
Fannonin Horaswa
Makarantar tana horaswa a fannoni kamar haka:
1. Rayuwa da girma cikin ruhaniya.
2. Ilimi da Tauhidin Littafi Mai Tsarki.
3. Dabaru da hanyoyin aikin bishara cikin al’adu.
4. Rayuwar yau da kullum a akin bishara.
Cancantar Shiga Makarantar
Maya haifuwa cikin Kristi, Tabbacin kira zuwa aikin bishara, Iya
Karatu da rubutu, Akalla shekara uku bayan tuba.
Neman Shiga Makarantar
Sai a amshi Takardar neman Shiga makarantar a makaratar a Kauna.
Naira Dari biyu (#200) ne kaccal.